Wani bam ya kashe sojoji a Libya

Fashewar bam a Libya

Wani bam da aka dana a mota ya tarwatse a gaban wani sansanin soja, a birnin Benghazi da ke gabashin Libiya.

Bam din ya kuma kashe akalla sojoji takwas.

Wasu mutanen goma kuma sun sami raunuka.

Bam din ya tashi ne yayin da jama'a ke watsewa daga wani bikin yaye jami'an soja a barikin.

Harin shine na baya-baya a jerin hare-haren da aka kai a ciki da kewayen birnin na Benghazi.