Boko Haram: Taro kan tsaro a tafkin Chadi

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasashen sun hada da Nijar, Kamaru, Najeriya da kuma Chadi

An bude taron manyan hafsoshin soji da ministocin tsaro na kasashen dake kewaye da tafkin Chadi a Yaounde na Kamaru.

Manyan kasashen dake kewaye da tafkin Chadi, na fuskantar kalubale daga kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram dake arewacin Najeriya.

Taron na kwanaki biyu zai tattauna batun kafa dakarun hadin gwiwa na kasashen, domin tabbatar da tsaro a kewayen tafkin na Chadi.

A ranar Talata ne ake sa ran samun sakamakon taron, wanda cikamako ne na taron da aka taba yi a Nijar game da rashin tsaro a yankin.