Kyautar dala miliyan daya ga malamin makaranta

Bill Clinton Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bill Clinton ne shugaban Gidauniyar Varky Gems

An bullo da wata sabuwar kyauta ta kasashen duniya, a bangaren ilimi.

Kyautar, wadda darajarta ta kai dala miliyan guda, za a bada ta ne ga duk malamin makarantar da yanzu haka yake koyarwar, wanda kuma ya kawo gagarumar gudunmawa ga sana'ar malantar.

Shekaru goma za a dauka ana ba wanda ya lashe kyautar wadannan kudaden, amma da sharadin cewa, dole ya cigaba da malantar har tsawon a kalla shekaru biyar.

Kyautar, wadda Gidauniyar Varkey Gems ta kaddamar, tana da goyon bayan jagoran Dubai, Sheikh Mohammed bin Rashid al Maktoum.

Shugaban gidauniyar na karamci, tsohon shugaban Amirka Bill Clinton, ya ce yana da mahimmanci matuka a jawo mutanen da suka fi hazaka ga fannin koyarwa, sannan kuma a girmama su da kyau.