2015: Kotu ta yi watsi da kara kan Jonathan

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Jonathan da Cif Obasanjo na takun-saka kan 2015

Wata babbar Kotun Tarayya dake zaman ta a kaduna, ta kori karar da wasu suka shigar gabanta suna kalubalantar cancantar shugaban Nigeria Goodluck Jonathan na tsayawa takara a shekarar 2015.

Alkalin kotun ya kori karar a bisa cewa masu karar ba su da wani dalili na kai kara domin shugaban bai ayyana aniyar sa ba.

A cewar kotun, Mr Jonathan a matsayin sa na shugaban kasa ya na da kariyar tsarin mulki da ta hana a tuhumashi.

Masu karar dai na cewa za su daukaka kara zuwa kotun na gaba.

Watanni shidda aka kwashe ana wannan shari'ar.

Karin bayani