Bani da manufa kan taron kasa- Jonathan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jonathan na shan suka game da taron kasa

Shugaban Nigeria, Dr Goodluck Jonathan ya kaddamar da taron kwamitin kasa a Abuja, babban birnin kasar.

A jawabinsa na bude taron, shugaban ya ce bai da wata bukata a boye da yake son cimma a wannan taron.

Mr Jonathan ya bukaci wakilan taron sun tattauna batutuwan da za su ciyyar da kasar gaba.

Wakilai kimanin dari biyar ne suke halartar taron, wanda zai tattauna a kan batutuwa daban-daban da suka shafi kasar.

'Yan adawa sun kaurace taron, inda suka ce bata lokaci ne kawai da barnata dukiyar al'umma.

Rahotanni sun nuna cewar za a kashe kusan naira biliyan bakwai a cikin watanni uku da za a shafe ana taron.

A watan Oktoban bara ne dai Shugaba Goodluck Jonathan ya ce za a yi taron kuma tun a lokacin ne batun ke ta janyo kace na nace.

Karin bayani