'Za a kashe naira biliyan 7 a taron kasa'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Jonathan na shan suka game da taron kasa

Batun ware naira biliyan 7 domin gudanar da taron kasa da za a fara a Nigeria na ci gaba da janyo cece-kuce.

Wasu 'yan kasar na ganin kudaden tamkar barnar dukiyar kasa ce, saboda a ganinsu taron ba zai kawo babban sauyi ba ga cigaban kasar.

Wasu rahotanni sun ambato wani babban shugaban Kirictoci a Nigeria, Bishop Mathew Hassan Kuka na bayyana kudaden da barnatar da dukiyar kasa.

Sai dai wasu na ganin taron zai yi tasiri wajen nemo bakin zaren dangane da wasu muhimman batutuwa da suka addabi kasar.

Bayanai sun nuna cewar wakilai 492 da za su halarci taron na tsawon watanni uku, kowannensu za a kashe masa fiye da naira miliyan 10.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar matsalar tsaro a kasar, da kuma rashin aikin yi a tsakanin matasa.

Karin bayani