PDP ta zargi Lamido da ba jam'iyyar APC kudi

Ahmed Adamu Mu'azu Hakkin mallakar hoto muazu facebook
Image caption Ahmed Adamu Mu'azu shugaban jam'iyyar PDP

Jam'iyyar PDP mai mulkin Nigeria ta zargi gwamnan babban bankin kasar da aka dakatar Malam Sanusi Lamido Sanusi da bai wa jam'iyyar APC da 'ya'yanta makudan kudade ba bisa ka'ida ba.

A wata sanarwa da PDP ta fitar, ta ce tana da kwararan shedu da ke nuna cewa wasu manyan jam'iyyar ta APC sun amfana da makudan kudade da ake zargin tsohon gwamnan ya kashe ba bisa ka'ida ba.

Ta ce ciki har da ba da wasu kwangilolin dubban miliyoyin Naira ga wasu jiga jigan APCn.

To sai dai a nata bangaren jam'iyyar ta APC ta musanta zargin na PDP.