Zama na musaman a kan makomar Cremia

Alummar yankin Cremia Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Alummar yankin Cremia

Majalisar Dokokin Rasha ta na shirin wani zama na musamman da shugaban Majalisar dattawan Crimea, bayan da shugaba Putin na Rasha ya sanya hannu a wata doka da ta amince da matsayin Crimea a matsayin kasa me yancin kanta.

Wani shafin sadarwa na Intanet na kasar ta Rasha da galibi ke bayar da labarai na gaskiya, ya ce a nan gaba Mr Putin zai sanya hannu a wata yarjejeniya da shugaban Crimea domin yankin ya kasance wani bangare na Rasha.

Sai dai kuma fadar gwamnatin Rasha ta Kremlin ba ta tabbatar da labarin ba kawo yanzu ,amma shafin sadarwar ya ce za a yi yarjejeniyar ne gaban 'yan Majlisar dokokin ta Rasha.

Kuma kotun tsarin mulkin kasar sai ta duba yarjejeniyar kafin majalisar ta sanya mata hannu.

Wakilin BBC ya ce zuwa karshen wannn makon ake saran komai zai kammala