Kamara mai gano bacin ran matuki

Kamara mai gano bacin ran matuki

Masu bincike na aiki a kan wata kamara, wacce za a sanya ta a sitiyarin mota, domin gano ko direba na cikin bacin rai.

Masanan dake Switzerland sun ce, direbobin dake cikin bacin rai kan fusata nan da nan, kuma ba sa maida hankali a tuki.

Saboda haka suke ganin yana da muhimmanci a gano halin da mutum ke ciki, domin inganta bada kariya.

Inda suka bayyana cewa gwajin na'urar da aka yi, ya nuna alamun samun nasara.

Sai dai binciken bai burge wasu masu kare ra'ayin direbobi ba.

Masu binciken dake cibiyar kimiyya ta kasar Switzerland dake Lausanne sun ce, fasahar za ta iya tantance yanayin bacin rai kala biyu, wato fushi ko yanayi na harzuka.

Haka kuma wani amfani da na'urar za ta yi shi ne na gano gajiya da kuma lumshe ido.

An yi gwajin na'urar ta Peugeot Citroen a cikin ofis da kuma a cikin mota.

Tuni dai aka fara aiki da na'urar dake fahimtar yanayin fuskar mutum, musamman a fannin wasan kwamfuta.

Sai dai akwai sauran jan aiki kafin a kai ga amfani da na'urar.

Domin masu binciken sun ce sun fuskanci kalubale wajen tabbatar da cewa abin da na'urar ta nuna haka yake a zahiri, ganin cewa yanayin fuskar mutane ya banbanta kwarai da gaske.