BBC ta nemi afuwar jami'ar LSE

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Akwai dubban dalibai a London School of Economics

BBC ta nemi afuwar Jami'ar London School of Economics da kuma wani dalibin jami'ar saboda daukar hoton bidiyo a asirce da aka yi a bara a Koriya ta Arewa da aka watsa a shirye-shiryen BBC.

Bayan gudanar da bincike, mahukunta BBC sun ce an saba ka'idar aiki a kan yadda wakilin BBC ya yi sojar gona a matsayin dalibi, yayi balaguro tare da sauran dalibai inda ya dauki hotuna a asirce lokacin ziyarar a Koriya ta Arewa.

Ko da yake akwai hujja daukar hotunan amma dai BBC ta ce ba daidai bane da aka ki bayyanawa sauran daliban ainihin makasudin daukar hoton bidiyon.

BBC ta nemi afuwa saboda daya daga cikin iyayen daliban ya yi korafi a kan cewar ba a nemi izinin dan sa ba aka dauki hoton bidiyon.