Ghana na son taimakon Nigeria kan lantarki

Shugaban kasar Ghana John Mahama Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption karancin wutar ta kai ga rarraba wutar daga uguwa zuwa unguwa

Shugaban kasar Ghana, John Mahama ya tura ministan makamashinsa zuwa Nigeria, a wani mataki na kokarin kawo karshen karancin wutar lantarki a Ghana.

Ministan makamashin Ghana zai tattauna da hukumomin Najeriya, kan yadda Najeriyar za ta kara adadin iskar gas da take sayar wa Ghana, domin samar da isasshiyar wutar lantarkin.

Ghana ta dora alhakin karancin wutar lantarki bisa rashin samun iskar gas daga Najeriya ko kuma rashin samunsa a kan kari.

Ana samun karuwar masu amfani da wutar lantarki a Ghana, inda a bara aka samu karuwar kashi 12 bisa dari, lamarin dake sanya wa a dauke wutan lantarki na tsawon yini guda.