An kama mahara a Kenya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A baya Kenya ta gamu da harin 'yan kungiyar Al Shabaab

'Yan sanda a birnin Mombasa da ke gabar teku a Kenya sun ce sun kama wasu mutane biyu da suke yawo dauke da bamabamai biyu boye a mota.

'yan sandan sun ce, mutanen, daya dan kasar ta Kenya dayan kuma dan asalin Somalia, suna shirin kai hari ne a wani wuri da ba a fayyace ba.

Sun ce sun sami nasarar damke mutanen ne sakamakon tsegunta musu bayanai da aka yi.

Kafafen yada labarai na kasar sun ce, an tsaurara matakan tsaro sakamakon lamarin.