Walkiya da tsawa na kashe mutane

Image caption Mace-mace na karuwa saboda yawaitar walkiya

Bisa dukkan alamu walkiya da tsawa na kashe mutane tare da raunata wasu da dama a kasashe masu tasowa, kamar yadda kwararru a fannin hasashen yanayi suka bayyana.

Watakila adadin wadanda suka mutu sakamakon walkiya ya zarta yawan wadanda suka rasu sakamakon ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa da kuma fari.

Kwamishinan kula da hasashen yanayi a Uganda Micheal Nkalubo ya ce "Ana samun karuwar walkiya a cikin 'yan shekarunan saboda sauyin yanayi".

Hukumomi a Afrika ta Kudu sun bayyana cewar ana samun karuwar mace-mace da raunuka sakamakon walkiya.

Haka lamarin yake a yankin Kudu maso gabashin Asiya inda kwararru suka ce adadin mace-mace na karuwa saboda walkiya.

Wani kwararre a Malaysia Hartono Zainal Abidin ya ce "Lamarin yana karuwa a wannan yanki musamman a Cambodia da Vietnam da kuma Thailand".

Ana walkiya a duk dakika a duniya, kamar yadda masana suka ce.

Kuma a cikin shekaru goma da suka wuce, bincike ya nuna cewar an samu karuwar yin walkiya a Malawi da Swaziland da kuma Zimbabwe.