Taron kasa ya dauki harami a Nigeria

Shugaban Najeriya Good Luck Jonathan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsohon mai shari'a Idris Kutugi ne ke jagorantar taron

An fara taron kasa a Najeriya, yayin da ake ci gaba da samun ra'ayoyi daban-daban game da cacantar yin taron daga mahalarta.

A ranar Litinin ne Shugaba GoodLuck Jonathan ya bude taron, yana mai tabbatar da cancantar yin taron wajen lalubo kyakkyawar makoma ga kasar.

Taron dai zai tattauna dukkan batutuwa da suka addabi 'yan kasa, kama daga rabon arzikin kasa, rashin tsaro, rashin ayyukan yi, tsarin shugabanci na shugaban kasa ko firai minista da sauransu.

Sai dai batu daya da ba a yarda mahalarta taron 492 su tabo ba shi ne batun raba kasar ta Najeriya, a tsawon zamansu na watanni uku.