An dage zaman taron kasa a Nigeria

Image caption Wakilai 492 ne ke halartar taron a Abuja

Wakilan taron kasa a Abuja babban birnin Nigeria sun yi ganawarsu ta farko kafin a dage zaman, don ci gaba da taron a ranar Litinin mai zuwa.

Shugaban taron Idris Legbo Kutigi wanda ya yi jawabin bude taron ya sanar da dage zaman don baiwa wakilai damar kikkintsawa domin soma mahawara gadan-gadan.

A ranar Litinin ne Shugaba GoodLuck Jonathan ya bude taron, yana mai tabbatar da cancantar yin taron wajen lalubo kyakkyawar makoma ga kasar.

Taron dai zai tattauna dukkan batutuwa da suka addabi 'yan kasa, kama daga rabon arzikin kasa, rashin tsaro, rashin ayyukan yi, tsarin shugabanci na shugaban kasa ko firai minista da sauransu.

Sai dai batu daya da ba a yarda mahalarta taron 492 su tabo ba, shi ne batun raba Najeriya, a tsawon zamansu na watanni uku.

Za a kashe kusan naira biliyan bakwai a wajen gudanar da taron.

Karin bayani