Nigeria za ta kawar da ta'addanci ta lalama

Kanar Sambo Dasuki Hakkin mallakar hoto The Will
Image caption Wasu na ganin amfani da lalama zai taimaka wajen magance matsalar Boko Haram a Najeriya

Ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan sha'anin tsaro ya fito da wani shiri na amfani da lalama wajen kawar da ta'addanci a kasar.

Mai bai wa shugaban kasar shawara, Kanar Mohammed Sambo Dasuki ya ce za su hada gwiwa da bangarorin al'umma, domin hana mutane zama 'yan ta'adda a maimakon magance matsalar bayan ta faru.

Kanar Dasuki ya yi nuni da cewa yana da wuya a tantance 'yan ta'adda da wanda babu ruwansu, abin da ke sa wa a wasu lokutan, matakan soji kan shafi wanda bai ji ba bai gani ba.

Sau da dama dai ana zargin jami'an tsaro wajen wuce gona da iri a yunkurin kawar da 'yan ta'adda a kasar.