Putin ya kare matakin Rasha a kan Crimea

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An sanya hannu a yarjejeniyar hadewa tsakanin Rasha da Crimea

Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya kare matakin da kasarsa ta dauka a kan yankin Crimea.

A cikin wani jawabi ga masu fada a ji na Rasha a zauren St George a fadar Kremlin, Mr Putin ya ce shigar da Crimea a cikin yankin kan iyakokin kasar Ukraine a shekarar 1954 da kuma a karshen yakin cacar baki kuskure ne.

Shugaba Putin ya bukaci Amurka da ta daina abunda ya kira halayya da maganganu irin na zaman yakin cacar baki.

A karshen taron Firayi ministan Crimea, Sergei Aksyonov da kuma Kakakin majalisar dokoki, Vladimir Konstantinov sun sanya hannu tare da shugabannin Rasha don hade mashigin ruwan na tekun Bahar Aswad da Tarayyar Rasha.

Mataimakin shugaban Amurka, Joe Biden, yayi Allah wadai da matakin da Rashar ta dauka, wanda ya ce tamkar kwatar filaye ne.

Ma'aikatar harkokin wajen Ukraine ta ce, bata goyi bayan hadewar Crimea da Tarayyar Rasha ba, kuma ba za ta taba amincewa da hakan ba.

Ta ce, jawabin Shugaba Putin ya nuna cewa, Rasha barazana ce ga kasashen da suka waye da kuma tsaron duniya.

Karin bayani