Ma'aikatan mai a Nijar na yajin aiki

Matatar mai ta SORAZ Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Matatar mai ta SORAZ

Ma'aikata 'yan kasa na kamfanin SORAZ da ke tace man fetur a Jumhuriyar Nijar , sun fara wani yajin aikin gargadi na kwanaki biyu.

Ma'aikatan sun ce sun dauki matakin ne domin nuna rashin jin dadinsu da abun da suka kira rashin daidaiton albashi tsakaninsu da takwarorinsu 'yan China da ke aiki a matatar man ta SORAZ.

Koda a makon jiya ma dai ma'aikatan 'yan Nijar sun yi wani zaman dirishan na kwanaki 2, kan irin wannan korafi da kuma matakin da kamfanin ya dauka na korar wani shugaban kungiyar ma'aikatan.

Ma'aikatan dai sun ce idan ba su samu biyan bukata ba, to kuwa bayan wannan yajin aiki, za su kira wani karin yajin aikin na tsawon kwanaki da dama.

A shekarar 2011 ne dai matatar man ta Damagaram ta soma aiki da zummar samar da gangar mai dubu 20 a kowace rana; koda yake ya zuwa yanzu abin da take samarwa bai wuce ganga dubu 12 ba.

Kamfanin man fetur na China, CNPC dai ya mallaki kashi 60 daga cikin 100 na jarin kamfanin na SORAZ yayinda Nijar ta mallaki kashi 40 daga cikin 100.

Karin bayani