'Yan tawayen Syria na aikata kisan gilla

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dubban mutane sun mutu sakamakon rikicin Syria

Sabbin bayyanai game da batun keta hakkin bil'adama a Syria sun nuna cewa, kungiyoyin 'yan tawaye na aikata kisan gilla a kan mutane dayawa.

Masu bincike na majalisar dinkin duniya sun gano kashe-kashe dayawa da suka ce irin na gilla ne - ciki har da a wani asibitin kananan yara a birnin Aleppo.

Tawagar Majalisar ta kuma ce, dakarun gwamnati sun kara yawaita hare-hare da bam mai kwanso, wanda jiragen sama ke jefawa.

A cewar jami'an, wani salo ne na neman firgita fararen hula.

Karin bayani