Rasha ta gargadi kasashen Yamma

Sergey Lavrov da John Kerry Hakkin mallakar hoto
Image caption Sergey Lavrov da takwaransa John Kerry na Amurka

Rasha ta gaya wa Amurka cewa ba za ta lamunta da takunkumin kasashen yammacin duniya ba a kanta game da Crimea.

Kuma ta yi barazanar mayar da martani kakkausa.

Ministan harkokin kasashen wajen Rasha, Sergei Lavrov, shi ne ya yi gargadin, a wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Amurka, John Kerry.

Yayi gargadin ne sa'oi bayan da shugabannin Rasha da na Crimea , suka sa hannu a kan wata yarjejeniya da ta amince da shigar da tsibirin cikin tarayyar Rasha.