Kamaru za ta tura da dakarunta zuwa tafkin Chadi

Shugaba Paul Biya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Paul Biya

Gwamnatin Kamaru za ta tura da sojoji 700 zuwa yankin kasashen da suka kafa hukumar tafkin Chadi domin tabbatar da tsaro a wurin.

Gwamnatin kasar ta bayana haka ne a taron da shirya a kan tabbatar da tsaro a yankin.

Ministocin tsaro na kasashen yankin sun tattauna akan neman hadin gwuiwa a tsakaninsu domin su samarwa al'umomin yankunansu rayuwa a cikin kwanciyar hankali

Bayanai sun ce kasashen Nigeria , Chadi, Jamhuriyar Niger da Camaru sun cinma yarjejeniya akan wasu abubuwa ko da yake an samu sabani a kan wasu batutuwa.