'Yan gudun hijira na fama da yunwa -kungiyar likitoci

Rikicin Jamuriyar Afrika ta tsakiya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rikicin Jamhuriyar Afrika ta tsakiya

Kungiyar likitoci ta Medicines San Frontiers ta yi gargadi akan halin da 'yan gudun hijira ke ciki wadanda suka tsere daga Jamhuriyar Afrika ta tsakiya .

Wani likita a sansanin 'yan gudun hijira na Sido dake makwabtaka da Chadi inda 'yan gudun hijira fiye da dubu 13 ke samun mafaka ya ce fiye da rabi daga cikin mutanen da ke yake kula da lafiyarsu na fama da yunwa.

Wani likitan ya kuma ce yara na zuwa da ciwo a ka sakamakon sararsu da aka yi da gatari.

Kungiyar ta ce rikicin ya tilastawa mata da dama shiga karuwanci domin kula da 'yayansu

Kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya ta rika fuskantar tashe- tashen hankulan tun bayan juyin mulki da akayi a watan Maris na shekarar da ta gabata.