Turkiyya ta musanta jigilar makamai Nigeria

Jiragen Turkiyya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Arewacin Nigeria na fama da tashin hankali na Boko Haram da 'yan fashi

Kamfanin zirga-zirgan jiragen sama na Turkiyya ya musanta zargin jigilar makamai ga wasu da ba a san ko su wanene ba a Nigeria.

A wata sanarwa da kamfanin ya aike wa kamfanin dillacin labarai na AFP, kamfanin jiragen ya ce ba ya jigilar makamai zuwa kasashen da basu da tartibin shugabanni ko kuma wadanda ke cikin yaki.

A ranar Talatar da ta wuce ne aka sanya wata murya a shafin intanet na You Tube, inda aka yi zargin muryar wani jami'in kamfanin jiragen Turkiyyan ne, Mehmet Karatas na shaida wa mai bai wa firai ministan Turkiyya Recep Tayyib Erdogan shawara cewa yana nadamar jigilar makaman.

Maganar wacce za ta iya shafar martabar kamfanin jiragen Turkiyyan na cikin jerin muryoyin da aka nada da ke goga kashin kaji ga Erdogan, gabannin zaben da za ayi a karshen watannin a kasar.