Satar bayanai: an sake gano Amurka

Hakkin mallakar hoto
Image caption A tsarin ana iya daukar duk maganar da aka yi ta waya a wata kasa a adana ta tsawon kwanaki talatin

Rahotanni a kafafen yada labarai na Amurka na cewa Hukumar Tsaro ta kasar ta kirkiri wani tsari na nadar maganganun jama'a a ko wace kasa.

Jaridar Washington Post ta ce,tun shekaru biyar da suka wuce ne aka fara amfani da tsarin.

Sai dai naurorinsa sun cika makil da maganganun wayoyin da aka nada na dubban miliyoyin jama'a a shekara ta 2011.

Jaridar ta danganta rahoton nata ne ga bayanan tattaunawar da aka yi da mutanen da suke da masaniya game da tsarin.

Da kuma takardun bayanan sirrin da tsohon jami'in leken asirin na Amurka da ya tsere, Edward Snowden ya fitar.

Mai magana da yawun fadar Amurka, Jay Carney, ya ki bayar da karin bayani kan lamarin, wanda kungiyoyin kare hakkin bil'adama suka kira me ta da hankali