An saba ka'ida wajen gyara gidan Zuma

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Zuma na fuskantar kalubale kan zaben dake tafe

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Afrika ta Kudu ta caccaki Shugaba Jacob Zuma kan amfani da kudin gwamnati wajen yi wa gidansa kwaskwarima.

A cikin rahoton, babbar jami'ar hukumar, Thuli Madonsela ta ce Shugaba Zuma ya saba ka'ida wajen amfani da dukiyar al'umma wajen gyara gidansa dake kauyensu.

Kafafen yada labarai a Afrika ta Kudu sun ce an yi amfani da wani bangare na kudin wajen kawata gidan shugaban kasar da abubuwan ba basu dace ba.

Wakilin BBC ya ce wannan rahoton zai iya janyo wa shugaba Zuma da jam'iyyarsa ta ANC cikas a yayinda ake shirin zabukan kasar a makwanni shida masu zuwa.

Karin bayani