Musayar kalamai tsakanin Rasha da Amurka

Vitaly Churkin na kasar Rasha Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Vitaly Churkin

An tayar da jijiyoyin wuya a wani zama na kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya tsakanin Rasha da Amurka.

Haka kuma kasashen duniya sun yi kakkausar suka ga yunkurin Rasha na mayar da yankin Crimea karkashinta.

Jakadan Rasha a Majalisar, Vitaly Churkin ya ce, al'ummar Crimea sun bayyana ra'ayinsu, sun kuma yi amfani da damarsu ta zaba wa kansu makomar da suke so.

Yayin da ita kuma jakadiyar Amurka a Majalisar, Samantha Power ta mayar da martani da cewa, kuri'ar jin ra'ayin da aka yi a Crimea, shirme ne kawai.

Jakadun kasashen biyu na yi wa juna kallon hadarin kaji, yayin da Babban Sakataren Majalisar dinkin Duniyar ke shirin zuwa Moscow domin tattaunawa da Shugaba Putin, domin samun mafita ta diflomasiyya kan rikicin.