Za a gina katafaren Dam a Congo

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Aikin shi ne mafi muhimmanci na raya kasa a Afrika a karni na 21 in ji Firai minista Augustin Matata

Bankin Duniya ya amince da bai wa Jamhuriyar Dumokradiyyar Congo dala miliyan 73 domin taimaka mata gina wata madatsar ruwa ta samar da wutar lantarki.

Bankin ya ce za a yi amfani da kudin ne hadi da wasu dala miliyan 33 na Bankin raya kasashen Afrika wajen gudanar da bincike kan tasirin madatsar ruwan ta Inga kan muhalli da kuma tabbatar da ganin cewa abu ne da zai dore.

Wasu manyan kamfanoni uku na duniya suna fafutukar neman samun kwangilar gina wani sashe na fadada madatsar ruwan, da ake cewa Inga Three.

Firai ministan Congon, Augustin Matata Ponyo , ya ce aikin zai matukar inganta rayuwar jama'a da ayyuka.