Kotu a India ta samu maza 4 da laifin fyade

Mata na zanga-zangar nuna adawa da fyade Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Lamarin ya janyo fushin al'umma a Delhi a shekarar 2012

Wata kotu a birnin Mumbai na India, ta samu wasu maza hudu da laifin aikata fyade a kan wata 'yar jarida a bara.

Gungun maza biyar ne suka afkawa 'yar jaridar mai shekaru 22, yayin da take daukar hoton wata masana'antar yin tufafi da ba a kammala ba.

Yayin da shi kuma abokin aikinta da suke tare, gungun suka yi masa duka suka daure shi.

A ranar juma'a ne kotun za ta yanke wa maza hudun hukunci, yayin da na biyar din ake shari'arsa a kotun kananan yara.