Dalibai sun yi zanga-zanga a Yamai

Kakakin majalisar dokokin Nijar, Hamma Amadou Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Kungiyar dalibai ta kasa, USN ta ce zanga-zangar ta shafi kasar baki daya

A Jumhuriyar Nijar, dubban dalibai ne na jami'ar Abdu Mummuni Diofo da makarantun Sakandare na birnin Yamai, suka yi zanga-zanga a gaban majalisar dokokin kasar.

Daliban na nuna bacin ransu ne a game da abin da suka kira, rashin kulawar da mahukuntan kasar ke ba bangaren ilimi.

Matsalolin da daliban suka ce suna fama da su, sun hada da rashin isassun ajujuwa da karancin kujerun zama da cibiyoyin kula da lafiyar daliban da dai sauransu.

Gwamnatin Nijar ta kafa wani kwamiti, domin duba matsalolin daliban da nufin warware su.