Taron kasa: Wakilan arewacin Nigeria na taro

Shugaban Najeriya da mahalarta taron kasa
Image caption An dage taron kasa zuwa ranar litinin mai zuwa

A Najeriya mahalarta babban taro daga arewacin kasar, za su yi wani taro da nufin daidaita irin bukatun da suka shafi lardinsu.

Taron na ranar Alhamis na neman yadda yankin arewacin, zai je zauren babban taron kasar da murya daya.

Wasu dattawan arewacin Najeriyar dai na da yakinin cewa, kowane bangare na kasar na da irin bukatun da yake ba fifiko.

A waje daya kuma kungiyar lauyoyi ta Najeriyar ta sanar da janye wa daga taron kasar, bisa korafin wakilcinta da aka ba mutum daya a taron.