Karin takunkumi a kan Rasha

Shugabannin kungiyar kasashen Turai Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugabannin kungiyar kasashen Turai

Kungiyar kasashen Turai ta EU, ta kara takunkumin da ta sanya wa Rasha sakamakon mayar da Crimea da Rashan ta yi karkashinta.

Shugabannin kungiyar ta EU da ke taro a Brussels, sun kara jerin sunayen jami'an gwamnatin Rasha da Crimea 11 akan guda 21 na farko da suka sanya wa takunkumin hana takardun shiga kasashensu da kuma rike ko dakatar da dukiyarsu.

An kuma bukaci shugabannin gamayyar kasashen Turan da su shirya sanya wasu manyan takukumin na tattalin arziki idan rikicin na Ukraine ya kara kamari.

Tun da farko dai Amurka ta sanar da sanya takunkumi a kan 'yan Rasha 20 wadanda na hannun daman shugaba Putin ne.

Sai dai ita ma Rashan ba tare da wani bata lokaci ba, ta sanya takunkumin hana shiga kasarta akan wasu manyan jami'an Amurka tara, da suka hada da tsohon dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar Republic John McCain.

Karin bayani