Ana ci gaba da kashe mutane a Darfur

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan sa kai a Sudan

Kungiyar kare hakkin bil-adama ta Human Rights Watch ta ce an karkashe mutane da dama a cigaba da tashin hankalin da ake yi a yankin Darfur na yammacin Sudan.

Kungiyar ta ce shugabannin kabilu a wasu kauyuka 2 sun gabatar ma ta da jerin sunayen fararen hula kusan 40 da aka hallaka a cikin 'yan makonnin da suka wuce a jerin artabu da aka yi tsakanin dakarun 'yan tawaye da sojojin gwamnati.

Kungiyar ta Human Rights Watch ta ce an kai hari a kan wasu karin kauyuka da dama, wasu daga cikinsu an yi ma su ruwan bama-bamai ne.

A halin da ake ciki kuma, kungiyar agaji ta Red Cross ta ce an kashe wani ma'aikacinta a lardin na Darfur.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce a cikin wannan shekarar kadai, mutane fiye da dubu dari 2 ne suka fice daga muhallinsu a lardin na Darfur.

Karin bayani