Majalisar Wakilai za ta binciki Diezani

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ministar man fetur, Diezani Alison- Madueke

Majalisar wakilan Nigeria za ta gudanar da bincike a kan zargin an kashe wa ministar man fetur ta kasar, Diezani Alison-Madueke, Naira biliyan goma, wajen kula da jirgin samanta na kanta.

Rahotanni sun ce an kashe kudaden ne a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Dan majalisar wakilai daga jihar Lagos, Samuel Adejare wanda ya gabatar da kudurin ya yi zargin cewar ana kashe kusan naira miliyan 130 a duk wata wajen lura da jirgin saman, wanda ya ce ministar tana amfani da shi ita da iyalanta ba don aikin gwamnati ba.

Majalisar wakilan za ta kwashe makwanni uku tana gudanar da binciken.

Karin bayani