Nigeria ta ware N10 biliyan na yaki da hamada

Sahara Hakkin mallakar hoto t
Image caption Sahara na shiga birane tana ta da kauyuka da dama a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta bayar da Naira miliyan dubu 10 domin dasa itatuwa, a yunkurinta na magance matsalar gusowar hamada.

Ministar muhalli ta kasar, Laurenshia Mallam ce ta bayyana haka a Abuja, a lokacin wata gana wa da kwamishinonin muhalli na jihohi 11 da ke fama da matsalar.

Ta ce a karkashin shirin mai suna Great Green Wall Project, ko GGWP a takaice, ana sa ran farfado da kusan hectare 22, 000 a jihohin.

Shirin zai bai wa kasashe 11 da suka hada da Najeriya, damar samar da wani bango na bishiyoyi me tsawon mil 4,300 da kuma fadin mil tara a fadin nahiyar Afrika daga Djibouti zuwa Senegal.