Arewa na so a cire rigar kariyar shugabanni

Mahalarta babban taron kasa
Bayanan hoto,

Wasu 'yan arewan na ganin talauci, cin hanci da rashin tsaro na cikin manyan matsalolin yankin

Mahalarta babban taron kasa daga arewacin Najeriya, sun yanke shawarar mika bukatar cire rigar kariya ga wasu shugabanni a taron.

Bukatar na daga cikin wasu muhimman bukatu da suka dunkule, domin gabatar wa a wajen babban taron kasar, a wani taro na daban da kungiyar tuntuba ta dattawan arewa ta shirya musu a Abuja.

Malartan kuma za su nemi a soke fifikon da ake bai wa jihohi masu arzikin mai, wajen rabon arzikin kasa daga cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Haka kuma sun amince za su nemi gwamnati ta gaggauta shawo kan matsalar tsaro da ta addabi yankin.

A ranar Litinin ne ake sa ran zauren babban taron zai fara zama gadan-gadan.