Mutane 3 sun mutu a rikicin a Filato

Gwamnan jihar Plateau, Jonah Jang Hakkin mallakar hoto plateau state govt
Image caption An kwashe fiye da shekaru goma al'umomin biyu na ga maciji da juna

Rahotanni daga jihar Filato a Nigeria na cewa, an shiga yini na uku a wani mummunan tashin hankali tsakanin mutanen yankin Shiwer da na yankin Dok-Pai.

Al'umomin dake kananan hukumomin Pankshin da Kanke, na rikicin ne bisa wani babban filin noma dake tsakanin yankunansu, da kowane bangare ke ikirarin mallakarsa.

Wasu bayanai dai na cewa arangamar tsakanin al'umomar, Angasawa wato 'yan-kabilar Ngas, da kuma 'yan kabilar Pai, ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma kona dimbin gidaje a cikin kauyuka.

Bayanai sun nuna cewa wata kotu ta taba yanke hukunci a kan filin, inda ta ce hukumar shata iyakoki ta Najeriya ce zata iya raba gardamar, abin da bai samu ba kawo yanzu.