Putin ya sa hannu a dokar hadewa da Crimea

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Putin da mkwarrabansa

Shugaba Putin na Rasha ya sa hannu a wata doka dake tabbatar da matakin da kasar ta dauka na hadiye yankin Crimea daga Ukraine.

Matakin na zuwa duk da karin takunkumin da Amurka da kuma Tarayyar Turai suka saka ma ta.

Sai dai Mr Putin ya ce Rasha ba za ta maida martani ga sabbin takunkumin ba.

Tun da farko Tarayyar Turai ta sa hannu a wata 'yarjejeniya da Ukraine, wadda za ta bada damar karfafa dangantaka tsakaninsu ta fuskar siyasa da tattalin arziki.

Tuni dai darajar hannayen jari a kasuwannin kasar ta Rasha, ta fadi da kashi 3 daga cikin 100 a cikin sa'o'in farko da fara hada-hada a kasuwannin, sakamakon sanarwar saka takunkumin.

A halin da ake ciki kuma, Faransa ta yi tayin tura jiragenta na yaki zuwa Poland da kuma kasashen yankin Baltic, da nufin karfafa sintirin da kungiyar tsaro ta NATO ke yi a yankin.

Karin bayani