An yi taron Musulmi da Kirista a Benue

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Rikici tsakanin 'yan kabilar Tibi da Fulani ya ta'azzara a baya bayan nan

A Nigeria, shugabannin addini da na al'ummomi da kuma jami'an tsaro sun gudanar da wani taron hadin gwiwa na yini biyu a garin Makurdi, babban birnin jihar Benue.

An gudanar da taron ne sakamakon yadda suka ga rikicin da ke afkuwa tsakanin Fulani makiyaya da manoma 'yan kabilar Tibi a jihar ke neman rikidewa ya zama rikicin addini.

Mahalarta taron sun tattauna, kuma sun kulla yarjejeniyar da za a yi amfani da ita wajen shawo kan matsalar.

Madakin Makurdi Alhaji Sallau Bello AbdurRahman na daya daga cikin wadanda suka shirya taron kuma ya shaidawa BBC cewa ana fatan samun masalaha ta hanyar wannan taron.