Nigeria: Mutane 17 sun mutu a Borno

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan kungiyar Boko Haram sun kaddamar da hare hare a Borno a baya bayan nan

Rundunar 'yan sanda a jihar Borno mai fama da rikici ta ce akalla mutane goma sha bakwai ne su ka rasu sakamakon fashewar wani abu a wata kasuwa dake jihar.

Rahotannin farko dai sun ce akalla mutane 29 ne suka mutu sakamakon fashewar abinda wasu suka kira makamin roka da aka harba kan kasuwar kauyen Nguro Soye da cikin yankin Bama ranar Alhamis.

Kwamishinan 'yan sandan jahar ya shaidawa BBC cewa har yanzu ba a iya tabbatar da abinda ya fashe a kasuwar mai ci kowanne mako ba.

Wannan yanki dai na daga cikin yankunan da sojojin Nigeria ke yaki da 'yan kungiyar nan ta Boko Haram.