An kaiwa musulmi hari a Bangui

Musulmi na tserewa a birnin Bangui Hakkin mallakar hoto AFP

Wasu musulmin da ke neman mafaka a wani masallaci a birnin Bangui dake Jumhuriyar Tsakiyar Afrika, sun ce 'yan kungiyar anti Balaka sun kai masu hari.

Daya daga cikin wadanda ke neman mafaka a masallacin ya shaidawa BBC cewa an kashe masu mutane huddu a harin.

Dubban mutane ne suka tsere daga kasar tun bayan tashin hankalin addinin kasar.