Nigeria: An gano masu niyyar sayar da jarirai

Hakkin mallakar hoto

Rudunar 'yan sandan Nijeriya ta ce, ta gano wani gida a kusa da Lagos inda aka ajiye mata su haihu domin a sayar da jariran da suka haifa

'Yan sandan sun ce, suna gano gidan ne a yankin Akute dake jihar Ogun, inda aka samu 'yan mata takwas dauke da ciki.

Yawancin 'yan matan dai 'yan kasa da shekaru 20 ne, kuma sun ce, za a sayi jaririn na su ne akan naira 300,000.

Tuni dai aka kama wanda yake da gidan da aka gano 'yan matan.

Matsalar ajiye 'yan mata masu juna biyu domin sayar da jariransu ta yi kamari a kudu maso gabashin Nijeriya.

Tun daga shekara ta 2011 'yan mata 125 ne jami'an tsaro suka kuɓutar daga irin wannan hali a Nijeriya.