Rasha ta kwace sansanin saman sojin Ukraine

Hakkin mallakar hoto
Image caption Dakarun Rasha sun yi amfani da motoci masu sulke da kuma gurneti

Dakarun Rasha a yankin Crimea sun kwace daya daga cikin manyan sansanonin soji na karshe da ke karkashin ikon Ukraine.

Dakarun na Rasha sun yi amfani da motoci masu sulke da kuma gurneti ne wurin afkawa sansanin mayakan sama na Belbek da ke daura da birnin Sevastopol na Crimea, inda sojojin Ukraine suka ki mika wuya a baya.

An jikkata akalla soja guda kafin kwamandan sansanin ya ba umarci dakarunsa da su ajiye makamansu su fice.

Wakilin BBC a Crimea ya ce yanzu ya rage ga sojojin su zabi yin biyayya ga Rasha, ko kuma su fice daga yankin har abada, wani abu da zai zamo mai wahalar gaske ga mafi yawan sojojin.