Faransa: Jam'iyyar masu ra'ayin rikau ta taka rawa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zabe sun nuna rashin gamsuwarsu da jam'iyyar Socialist mai mulki

Jam'iyyar masu tsananin ra'ayin rikau ta Faransa, National Front ta samu nasara fiye da yadda aka yi tsammani a zagaye na farko na zaben kananan hukumomi a fadin kasar

Hakan na zuwa ne yayin da masu zabe ke nuna rashin gamsuwarsu da jam'iyyar Socialist mai mulki, ta shugaba Francois Hollande.

National Front ta samu rinjaye a garin Henin-Beaumont da ke arewacin kasar wanda a baya ya saba zabar masu ra'ayin kawo sauyi.

A wasu garuruwan dari biyu kuma da ke fadin kasar, 'yan takarar National Front sun yi nasarar kai wa zagaye na biyu na zaben.