Tasirin kaurace wa taron kasa a Nigeria

Image caption Kungiyar lawyoyi ta Nigeria ta sanar da janyewar ta daga taron

Masu sharhi na ganin kaurace wa taron kasa, da kungiyoyi kamar ta lauyoyin Nigeria suka yi, zai janyo koma baya ga taron.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da mahalarta babban taron, za su fara tafka muhawara a ranar Litinin.

Baya ga wasu daidaikun mutune da suka sanar da kaurace wa taron, kungiyoyi kamar ta lauyoyi ta kasar da ta malamn jami'a sun kaura cewa taron.

Sai dai shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya nuna muhimmancin yi taron, domin nemo mafita ga matsalolin da suka addabi 'yan kasar.