Saudiyya ta ja kunnen 'yan India dake ƙwadago

Hakkin mallakar hoto AFP Getty images
Image caption Abdallah, sarkin Saudiyya

India ta gargadi 'yan kasar ta dake kasar Saudiyya da kada su yi yajin aiki saboda hukumomin Saudiyyar za su iya ɗaure su ko su maida su gida.

Ofishin jakadancin India a Riyadh ne yayi gargadin, a wata sanarwa bayan wasu 'yan kasar dake aikin shara a wani asibiti suka yi jayin aiki saboda anyi watanni 9 ba a biya su albashi ba.

Ofishin jakadancin Indiyar ya ce yana tattaunawa da ma'aikatan, da kuma kamfanonin da ya dauke su aiki don ganin an warware matsalar.