'Yadda 'yan Boko Haram suka tsare mu'

Image caption Liatu da Janet sun ce suna mugun mafarki

Wasu mata biyu da 'yan Boko Haram suka sace a yankin arewa maso gabashin Nigeria sun bada bayanan yadda rayuwarsu ta kasance a hannun 'yan kungiyar.

Liatu 'yar shekaru 23, ta bayyana cewar ta shafe kwanaki 12 a cikin dajin Sambisa tare da 'yan Boko Haram kafin ta kubuta.

Tace ta bar Maiduguri za ta je kauyunsu, ta fada hannun 'yan Boko Haram wadanda suka kashe hanya, suka kashe mutane suka tafi da wasu cikin daji.

Ga yadda ta gudu, ta ce "Wani mutumi yace mana sau daya ake mutuwa sai muka shiga mota, muka gudu, sai 'yan Boko Haram suka biyo mu a babur, suna harbi, suka kashe wadanda ke bayan motan. Da muka doshi garin Bama sai suka gudu".

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abubakar Shekau da mukkarrabansa

A cewar Liatu 'yan Boko Haram sun ce ta karbi addinnin Musulunci kuma ta auri daya daga cikinsu kuma a idonta suka kashe kusan mutane 50.

'Yanka wuya'

Ita kuwa Janet mai shekaru 19, 'yan Boko Haram sun tsare ta ne na tsawon watanni uku.

A cewarta, 'yan Boko Haram sun nemi sukata cikin mayakansu.

Tace "Sun je Gwoza sun dauko mutane biyar zuwa sansaninsu. Saka yayyakasu a gabana, suka ce min in yanka wani a makogwaro, sai na kasa, sai matar dayansu ta kashe mutumin."

Janet ta ce ta gane fuskokin yawancin mutanen Boko Haram din don makwabtansu ne.

A cewarta ta yi karyar ciwon ciki ne, ta samu ta kubuta.

'Kashe Matasa'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan Boko Haram sun kona makarantar suka kuma kashe mutane 30

Tun daga watan Fabarairu, an rufe makarantun sakandare kusan 100 a jihohin arewa maso gabashin Nigeria wato Borno da Yobe da kuma Adamawa.

Hakan ya biyo bayan kashe dalibai kusan 30 a kwalejin gwamnati dake Buni Yadi a jihar Yobe, wadanda 'yan Boko Haram suka kashe cikin dare.

Tun daga farkon wannan shekarar, 'yan Boko Haram sun kashe mutane fiye da 500.

Jihohi uku na arewa maso gabashin Nigeria na karkashin dokar ta-baci da shugaba Jonathan ya kafa, amma dokar ba ta kawo karshen zubar da jini ba.

Karin bayani