'Babu wanda ya rayu a jirgin saman Malaysia'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Iyalan wadanda ke cikin jirgin sun nuna bakin ciki

Firaministan Malaysia Najib Razak ya sanarda cewar jirgin saman nan da ya bace MH-370 ya fada cikin tekun India, kuma babu wanda ya tsira da ransa a ciki.

Ya shaidawa manema labarai cewar nazarin da kwararrun Birtaniya su ka yi daga hoton tauraron dan adam sun tabbatar da cewar jirgin saman Malaysia din, ya kife ne a cikin teku, nesa da kasa.

Ya bukaci kafafen yada labarai sun mutunta sirrin iyalan fasinjoji 239 da matuka jirgin da suka mutu, inda ya ce jiran sauraron bayanai na da tada hankali.

Jirgin saman MH-370 ya bace bat makwanni biyu da suka wuce bayan ya taso daga Malaysia za shi China.

Jiragen sama dana ruwa da dama ne daga kasashe daban-daban suka bazama wajen neman baraguzan jirgin.

A halin yanzu dai jiragen saman yaki na Australia suna kokarin dauko wasu abubuwa da ake zaton baraguzan jirgin saman ne.

Karin bayani