Microsoft na shiga email din jama'a

Microsoft ne ya mallaki shafin Hotmail

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Microsoft ne ya mallaki shafin Hotmail

Kamfanin Microsoft ya na fuskantar matsin lamba bayan ya amince yana karanta sakwannin email din mutanen dake amfani da Hotmail.

Microsoft ya ce ya karanta adreshin email din wani marubuci ne a kokarin gano wanda ke kwarmata bayanai ga marubucin a tsakanin ma'aikatansa.

Microsoft shi ke da shafin email din Hotmail wanda a yanzu ake kira Outlook.com.

Wani babban jami'in kamfanin John Frank ya ce "suna shiga shafukanne kawai a lokutan da ya zama tilas".

A cewarsa matakin Microsoft din bai sabawa doka ba.

Matakin na Microsoft ya biyo bayan wata shari'a da ake yi a Amurka a kan wani ma'aikacin kamfanin wanda ake zarginsa da baiwa wani mutumi bayanan sirrin kamfanin na Microsoft.

A yanzu dai ma sharhanta sun ce Microsoft ya bi sawun kamfanoni irinsu Google da Yahoo da Apple da ake zargin suna bin diddigan sakwannin email din aboka huddarsu.