Yara miliyan daya na kamu wa da tarin TB

Wata yarinya ana mata allurar tarin fuka Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption WHO ta ce kimanin mutane 1.3 miliyan sun mutu a dalilin tarin TB, a shekarar 2012

Wani sabon bincike na nuna cewa, ana samun yara kimanin miliyan daya dake kamuwa da cutar tarin fuka, duk shekara a duniya.

Hakan dai ya ninka adadin da ake tunani a baya, a cewar binciken da aka wallafa a mujallar kiwon lafiya ta Lancet, da ya zo daidai da ranar tarin fuka ta duniya.

Binciken ya gano cewa yara da dama suna mutuwa ba gaira ba dalili, saboda kashi daya cikin uku na cutar kawai ake gano wa.

Masu binciken sun ce cutar na saurin kama yara, saboda haka ana bukatar kayayyakin gwaji masu inganci, domin samun kulawar da ta dace.