'Gurbatacciyar iska ce babbar barazanar kiwon lafiya'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hukumar ta ce mata da kananan yara lamarin yafi shafa

Hukumar lafiya ta duniya, W.H.O ta ce gurbatar iska ita ce babbar barazanar da ke fuskantar kiwon lafiya a fadin duniya.

Sabon bincike ya nuna cewa gurbatacciyar iska ta halaka kimanin mutane miliyan bakwai a shekarar dubu biyu da sha biyu, inda mafi yawan mace-macen suka faru a kasashen Kudanci da gabashin nahiyar Asiya masu matsaikacin tattalin arziki.

Hukumar ta ce mata da kananan yara lamarin yafi shafa domin su na suka fi mu'amala da wutar girki.

Hukmar ta W.H.O ta kuma ce gurbatar iska a kan tituna babbar matsala ce a kasashen da ke samun bunkasar masana'antu cikin gaggawa irin su India da China.